Sukar da ake yi wa gwamnatin Isra'ila a cikin gida na ci gaba da karuwa bayan sanar da matakin mamaye Gaza. Amma kuri'ar jin ra'ayin jama'a, ta nuna cewa sukar ta fi alaka da neman a sako wadanda Hamas ke garkuwa da su.
Firaministan Isra'ila Benjamin NetanjahuHoto: Abir Sultan/AFP
Talla
Yayin da Isra'ila ke ci gaba da shirinta na mamaye Zirin Gaza gaba dayansa, gwamnatin Benjamin Netanyahu na fuskantar karin suka daga cikin gida. A karshen mako, Isra'ila ta shaida gagarumar zanga-zangar da ke zaman guda cikinwa wadanda aka taba yi kan yakin da take ci gaba da yi a Gaza, inda dubban Isra'ilawa suka fito kan tituna suna nuna bacin ransu. Har yanzu akwai kimanin Isra'ilawa 50 a hannun kungiyar Hamas a Zirin Gaza, kuma iyalansu suna jin tsoron cewa shirin Netanyahu na kwace iko da yankin zai kara jefa rayuwar 'yan uwansu cikin hadari.
Gil Dickmann dan uwan wata mata ce da ta mutu a hannun Hamas mai suna Carmel Gat ya shaida wa DW cewa, yanke shawarar mamaye karin kasa zai jefa rayuwar sauran wadanda Hamas din ke garkuwa da su da suka rage a hannunta cikin hadari. Ita ma Naama Shueka 'yar uwar matashi Evyatar David da ke hannun Hamas da aka gani a rame a wani bidiyo da Hamas ta fitar kwanan nan ta ce, hanya daya tilo da za ta dawo da su da rai ita ce cimma yarjejeniyar sako su. Sannu a hankali yawan Isra'ilawan da ke goyon bayan iyalan wadanda Hamas ke garkuwa da su na karuwa. Binciken da Cibiyar Dimukuradiyyar Isra'ila (IDI) ta gudanar, ya nuna yadda ra'ayin jama'a ya sauya.
Duk da gargadin da sojojin Isra'ila suka yi, dubban Falasdinawa da aka yi wa kawanya sun yi tattaki daga Kudu domin komawa arewacin Zirin Gaza.
Hoto: Ramadan Abed /REUTERS
Hijira daga Kudu zuwa Arewa
Dubban Falasdinawa sun yi tattaki ta gabar teku daga kudu zuwa arewacin Zirin Gaza. Sun dauki wannan mataki duk da cewa sojojin Isra'ila sun yi gargadin cewa har yanzu yankin Arewa na zama yankin da ake gwabza fada. Sai dai fatan janyewar sojoji a Arewa da fargabar kai farmakin soja a kudancin kasar ya sa su komawa gidajensu, duk da cewa an lalata su.
Hoto: Yasser Qudihe/Middle East Images/IMAGO
Yankunan da aka lalata
Yankuna da dama na Zirin Gaza ne sojojin Isra'ila suka lalata don mayar da martani ga mummunan harin ta'addancin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban 2023. Kusan rabin al'ummar yankin miliyan 2.3 sun guje wa fadan zuwa kudancin zirin. Amma da yawa sun fara komawa Khan Yunis, inda gine-gine da yawa suka lalace.
Hoto: Ali Jadallah/Anadolu/picture alliance
Takardun gargadi
Sojojin Isra'ila sun rarraba takardu domin yin gargadi ga mutane cikin harshen Larabci game da "yanki mai hatsari na yaki" a arewacin Gaza. Wasu iyalai da suka koma Beit Hanoun da Jabalia a makonnin da suka gabata, bayan janyewar sojojin Isra'ila, sun sake barin wurin saboda fargabar barkewar wani sabon fada.
Hoto: -/AFP/Getty Images
"Muna son gidajenmu"
Tun tsawon watanni, wadanda suka rasa matsugunansu suna zama a karkashin tantuna a sansanoni da makarantu da kuma gidajen dangi a kudancin Zirin Gaza. "Muna son gidajenmu, muna son rayukanmu, muna so mu koma, ko ba a tsagaita wuta ba," in ji wata mace da ake kira Ummu Nidhal Khatab a kan hanyarta ta komawa Arewacin Zirin Gaza.
Hoto: Yasser Qudihe/Middle East Images/IMAGO
Wahala, 'yunwa da rashin isasshen taimako
Halin da ake ciki na jin kai a Zirin Gaza yana da muni. Bayan watanni shida na yaki, kusan mutane miliyan daya na fama da 'yunwa. Akwai fatan cewa kayan agajin da ake harbawa ta sama za su iya rage wahalhalun da ke addabar arewacin zirin, sannan Isra'ila ta bude sabbin hanyoyin kai kayan agaji. Sai dai a cewar Majalisar Dinkin Duniya, yawancin kayan agajin ba sa kaiwa ga mutanen da ke bukata.
Hoto: Mahmoud Issa/dpa/picture alliance
Harbe-harbe a wani shingen bincike
Tafiya zuwa arewacin Zirin Gaza na da hadari. Shaidun gani da ido sun sanar da cewa, an yi harbe-harbe a wani shingen bincike da sojojin Isra'ila ke da iko a hanyar shiga yankunan arewaci. Asibitin Awda da ke tsakiyar Zirin Gaza ya ba da rahoton mutuwar mutane biyar tare da jikkatar wasu 54. Sojojin Isra'ila ba su ce komai kan wannan batu ba.
Hoto: Ramadan Abed /REUTERS
Mage a cikin jaka
Wani yaro ya kula da kyanwarsa a kan hanya mai hadari ta zuwa Arewacin Gaza. Yakin ya riga ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula Falasdinawa sama da 34,000, kuma akalla 13,000 daga cikinsu yara ne. Kimanin mutane miliyan 1.8 sun rasa matsugunansu. Gagarumar matsalar jin kai na shirin kunno kai, a daidai lokacin da wasu sassan yankin ke fuskantar yunwa. Ba a kai ga yarjejeniyar tsagaita wuta ba.
Hoto: Ramadan Abed/REUTERS
Hotuna 71 | 7
A tsakiyar watan Oktoban 2023, jim kadan bayan harin Hamas na bakwai ga Oktoba kan Isra'ila, kaso 17 cikin 100 ne kacal na Isra'ilawa suka ce gwamnati ta shiga tattaunawa domin sakin wadanda Hamas din ta kama ko da hakan na nufin a dakatar da fada. Amma shekara guda bayan harin, kaso 53 cikin 100 sun amince da irin wannan ra'ayin. Ko da yake mafi yawan Isra'ilawa suna so a dawo da mutanen da ke hannun Hamas ne da kuma ceton rayuwar sojojinsu, amma ba wai suna tausayin Falasdinawa ba ne ko kuma son kasancewa tare da su kamar yadda wani bincike ya gano. Wani binciken da Cibiyar Dimukuradiyya ta Isra'ila IDI ta gudanar a karshen watan Yuli a kan ko Isra'ilawan sun damu da halin yunwa da ake ciki a Falasdinu, ya nuna cewa kaso 79 cikin 100 ba su nuna damuwa ba.
Wani marubucin Isra'ila Etgar Keret ya shafe watanni yana zanga-zanga, kan abin da gwamnatin Netanyahu ke yi a Gaza ya kuma nuna farin ciki da ganin karin 'yan Isra'ila sun bi sahunsa. Keret ya kuma yi kokarin bayyana dalilin da yasa Isra'ilawa, ba su damu sosai da halin da Falasdinawa ke ciki ba. A cewarsa, irin labarai da ake yadawa a kasar a baya da kuma na makonnin nan sun sha bam-bam musamman a kan halin da ake ciki. Masu nazarin ayyukan kafafen yada labarai a Isra'ila suna jaddada cewa, kaso 40 cikin 100 na Isra'ilawa ne ke kallo labarai a talabijin. A yayin da kashi 78 cikin 100 ke amfani da shafukan sada zumunta, inda ake yada rahotanni da hotuna na halin da ake ciki a Gaza.