170810 Indien Pakistan
August 18, 2010Tsawon makonni biyu da suka wuce, ambaliyar ruwa ta mamaye fiye da kashi ɗaya cikin biyar na faɗin ƙasar Pakistan, yanayin da ke zama mafi tsanani da ƙasar ta fuskanta a tsawon tarihi. A lokacin wata ziyara da ya kai yankunan da wannan bala'i ya shafa, sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon, ya yi kiran samar da taimakon gaggawa na tsabar kuɗi Dala miliyan 460 domin taimakawa mutane miliyan 20 da wannan ambaliya ta shafa.Ita ma ƙasar India dake maƙwabtaka da Pakistan ta yi alƙawarin bada gudunmawar Dala milyan biyar, sai dai kuma Pakistan ɗin na nuna ɗari-ɗari wajen karɓar gudunmawar daga India. Ko menene ya yi zafi haka ?
Matsayin da gwamnatin Pakistan ta ɗauka akan wannan al'amari shine cewa batu ne mai sarƙaƙiya. Gudunmawar agajin gaggawa na Dala miliyan biyar India ta ce za ta baiwa maƙwabciyarta Pakistan kuma tsohuwar abokiyar gabarta domin taimakawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a kasar, sai dai har yanzu Pakistan ta ƙi baiyana aniyar karɓar wannan taimako. Dalili a cewar Sajjad Naseer masanin kimiyyar siyasa a birnin Lahore shine.
" Ƙin karɓar gudunmawar abu ne da ya shafi tunƙaho na alfahari da ƙasarka. A ɓangare guda ana iya cewa a yanayin da ƙasa ke cikin annoba, za ta iya yin maraba da kowane irin taimako daga ko ina komai ƙanƙantarsa. Sai dai kuma fa gwamnatin Pakistan na buƙatar tunani da yin nazari mai zurfi game da makomar hakan a siyasance, kafofin yaɗa labarai a Pakistan na ta yin sharhi kan dacewa ko akasin haka dama raunin shugabanci idan ta karɓi wannan taimako daga Indiya wanda suke gani zai iya zubarwa da gwamnatin martaba.
Ƙasashen biyu dai na Indiya da Pakistan masu ƙarfin makaman Nukiya duk da tsamin dangantakar dake tsakanin su a tsawon shekaru goma da suka wuce su kan taimakawa juna a duk lokacin da wata masifa daga Indallahi ta afkawa yar uwarta.
Misali a shekarar 2001 an sami aukuwar girgizar ƙasa a birnin Bhuj dake jihar Gujarat a ƙasar Indiya wanda ya hallaka mutane kimanin 25,000. A wancan lokaci Pakistan ta aika da taimakon kayayyaki da suka haɗa da Tantuna da abinci da kuma barguna.
Haka ma dai a shekarar 2005 an sami aukuwar girgizar ƙasa a yankin tsaunukan Pakistan a lardin Kashmir dake tsakanin ƙasashen biyu wanda ya shafi mutane kimanin 80,000. Indiya ta bada jirage masu saukar ungulu waɗanda za su riƙa jigilar ceto mutane daga kan tsaunukan.
Mutanen yankin na Kashmir dake ɓangarorin biyu sun haɗa kansu suka taimaka wajen sake gina yankin. Indiya ta bada gudunmawar tsabar kuɗi Dala miliyan 25. Sajjad Naseer masanin kimiyyar siyasa ya jaddada fa'idar irin wannan taimako a mawuyacin yanayi.
" Dangantaka tsakanin Indiya da Pakistan wajibi ne mu kalle ta, ta fuskoki guda biyu, na farko akwai dangantaka tsakanin gwamnati da gwamnati, duk da cewa suna zaman tankiya, to amma alaƙar dake tsakanin jama'arsu ta banbanta. Kusan shekaru 12-14 yan jarida da ƙungiyoyin farar hula daga ɓangarorin biyu kan ziyarci juna. Ko da a makon da ya gabata yan jaridar Indiya sun haɗu a birnin Lahore inda suka tara gudunmawa domin tallafawa waɗanda wannan ambaliyar ta shafa a Pakistan. Ka ga wannan abu ne mai kyau to amma fa sai idan waɗannan ƙungiyoyi sun yi ƙarfi ne za su iya tilastawa gwamnatocinsu yin sulhu domin kyautata dangantakar dake tsakaninsu.
Yaƙe yaƙe har uku aka gwabza tsakanin Indiya da Pakistan tun bayan da suka sami yancin kai a shekarar 1947. Yunƙurin baya bayan na samun zaman lafiya a tsakaninsu ya ci tura, musamman bayan harin da aka kai cibiyar kasuwancin Indiya a Mumbai a watan Nuwambar shekarar 2008.
Wani masanin harkokin tsaro na ƙasar Indiya Afsar Karim yace ya kasa fahimtar irin wannan hali na Pakistan.
" Wannan abin takaici ne ban san dalilin da zai sa a haɗa masifar da ta shafi al'uma da sha'anin siyasa ba".
Su ma dai wasu yan ƙasar Pakistan ɗin sun tofa albarkacin bakinsu da cewa " Ra'ayi na shine wannan abu ne da ya shafi taimakon jin ƙai, muna karɓar taimako daga sauran ƙasashen duniya me ya sa ba za mu karɓa daga Indiya ba ?.
Wannan kuwa cewa yake Indiya maƙwabciyarmu ce menene aibu idan mun karɓi taimako daga gareta ?.
Mawallafa : Priya Esselborn / Abdullahi Tanko Bala
Edita : Umaru Aliyu