1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

190813 Merkel Porträt

September 4, 2013

Basira da juriya da kuma hangen nesa, sun taimaka wa shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel wajen nuna bajinta a fagen siyasar kasar.

Von Endfrisur und Apricotblazer - Angela Merkels Outfitwandel: (v.l. oben 1995, 2001 nicht im Bild) und unten 2004 und 2005 (Bildkombo). Fotos: dpa +++(c) dpa - Report+++, Von ´Endfrisurª und Apricotblazer - Angela Merkels Outfitwandel: v.l. oben 1995, 2001 und unten 2004 und 2005 (Bildkombo). Fotos: dpa +++(c) dpa - Report+++.CDU; .Haarmode; .Personen; .Politik; Frisur; l‰cheln; neutral; "Christlich_Demokratische_Union CDU CDU"; Conservative; hair_styling; hairdo; hairdressing; hairstyle; neutral; People; POL; politics; smile; smiling
Hoto: picture-alliance/dpa

Duk da cewar, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ba ta yi fice ba irin na sauran shugabannin gwamnatin kasar da suka gabaceta ba yayin tasowarta, kuma karatun da ta yi ma, bai shafi na siyasa ba, amma kuma rawar da take takawa a fagen siyasar, na baiwa kowa mamaki. A yanzu dai za ta tsaya takarar neman tazarce a mukamin shugabar gwamnati a karo na uku kenan.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da manazarta ke kwatantawa da kallabi a tsakanin rauna, ta fito ne daga yankin gabashin Jamus mai bin tsarin kwaminisanci a lokacin yakin cacar-baka, kuma duk da cewar tana da ilimi mai zurfi na digirin digirgir a fannin Physics, amma tana ci gaba da nuna bajinta a fagen siyasar Jamus da ta runguma da tsakar rana, amma kuma tauraronta ke ci gaba da haskawa.

A matsayinta na mataimakiyar kakakin tsohon firimiyan Jamus Ta Gabas Lothar de Meiziere, Merkel, 'yar shekaru 35 a wancan lokacin, ta sami damar cin gajiyar kwarewa a harkar sadarwa. Ta kuma zama ministar muhalli a karkashin tsohon shugaban gwamnatin Jamus Helmut Kohl a shekara ta 1994, matsayin da kuma a ke ganin ya dace da ita bisa zurfin ilimin da take dashi a Physics.

Hoto: AFP/Getty Images

Ci-gaban da jam'iyyar CDu ta samu a karkashin Merkel

Bayan rasa madafun ikon da jam'iyyar ta ta CDU ta yi a shekara ta 1998, Merkel ta zama babbar sakatariyar jam'iyyar, kuma a tsukin shekaru 13 da ta yi tana jagorancin jam'iyyar, takwas daga ciki, tana rike da mukamin shugabar gwamnati, ba tare da 'yan adawa na cikin gida a jam'iyyar sun yi mata wata illa ba. Jacqueline Boyse, fitacciyar 'yar jarida da ta rubuta tarihin rayuwar Merkel, ta yi tsokaci a kan basirarta:

Ta ce "Tana da natsuwa wajen tattara hujjoji da kuma ra'ayoyi mabanbanta, sannan ta zartar da hukunci. Haka kuma tsarinta ya ke a ko da yaushe."

A dai yakin neman sake zaben Merkel - karo na uku a matsayin shugabar gwamnati, badakalar da ta shafi satar bayanan siriin jama'ar da hukumar leken asirin Amirka ta yi, wanda wani tsohon jami'in hukumar leken asirin ya fallasa, na zama zakaran gwajin dafi ba wai kawai ga manufofin ketare na Merkel ba, harma da na cikin gida, amma kuma kamar kullum, ta bi lamarin sannu a hankali, inda da farko ta yi shiru, sai kuma ta kyale masu magana da yawunta nuna kyamarsu, kana da karshe kuma ta bayyana matsayinta yayin wata hira da tashar telebijin:

Merkel ta ce "Ina ganin muna bukatar abubuwa biyu ne. Muna bukatar aikin leken asiri. Sannan na biyu, muna bukatar su martaba dokokin dimokradiyya wajen yin aikin, amma kuma alhaki ne da ya rataya a wuyan jami'an, su baje komi a fei-fei dangane da hanyar da suka bi wajen samun bayanan."

Hoto: Reuters

Rawar da Merkel ta taka wajen warware rikicin Euro

Jama'a dai na ganin tsarin da Merkel ke bi a matsayin wata baiwar siyasa ce da Allah ya hore mata, wadda kuma ta sa jama'a ke kaunarta. Sai dai kuma a tarihin kasancewarta shugabar gwamnati, ta fuskanci wasu lokuta da ke da wahala, musamman yayin rikicin kudin da wasu gamayyar kasashen Turai da ke yin anfani da takardar kudin Euro suka fada a ciki. Ralph Bollmann, marubuci, kana dan jarida a Jamus, ya ce a lokacin ma ta nuna bajinta:

Ya ce " Ta yi anfani da basira wajen gamsar da masu dari-dari da makomar Euro a Jamus da kuma aiwatar da mhimman sauye-sauye ga sha'anin tattalin arziki, duk da kalubalen da ta fuskanta daga jam'iyyun adawa a cikin gida."

Duk da koma bayan da jam'iyyar CDU - ta Merkel ta samu a wasu zabukan baya bayannan, Ralph Bollmann, ya ce akwai yiwuwar za ta yi nasara a wannan zaben ma.

Mawallafi : Jeanette Seiffert / Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe