EU ba za ta sauya yarjejeniyar Brexit ba.
December 12, 2018A lokacin da take jawabi a zauren majalisar dokoki ta Bundestag gabanin amsa tambayoyi daga wakilan majalisar, shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta jaddada matsayin kungiyar tarayyar Turai ta EU na dagewa kan yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga kungiyar wato Brexit, amma ta karfafa cewa har yanzu tana kan bakanta na ganin Birtaniya ta fice cikin tsanaki kamar yadda yarjejeniyar ta Brexit ta tanada.
"Ba mu da niyyar canja yarjejeniyar Brexit. Wannan shi ne matsayi na bai daya da dukkan membobi 27 na kungiyar EU suka dauka. Saboda haka, ka da a yi tsammanin samun wasu canje-canje a karshen mahawararmu."
Merkel ta kara da cewa har yanzu akwai lokaci na ficewar Birtaniyar a tsanake daga kungiyar EU tana mai cewa ko da yake lokaci na kurewa, amma duk da haka tana da kyakkyawar fatan cewa za a iya kaucewa fadawa cikin rudani a kan batun. Merkel wadda ta gana da Firaministan Birtaniya Theresa May a ranar Talata ta ce abubuwa na neman su dagule a birnin London.
"Muna ci gaba da aiki, ina kuma da fata za a rabu lami lafiya. Lokacin da ya rage kadan ne, amma duk da haka muna da lokaci. Firaministar Birtaniya ta zo Berlin a ranar Talata ta kuma ce za a kada kuri'a kafin ranar 21 ga watan Janairu mai zuwa. Kamar yadda kuka sani kuke kuma ji a kafafen yada labaru abubuwa na kunno kai a kullum. Abin da zan fada wa al'ummar Jamus shi ne muna aiki tukuru don samun Brexit mai kyau."
Har yanzu ana cikin duhu game da makomar 'yan Birtaniya mazauna Jamus da kuma makomar Jamusawa da ke zaune a Birtaniya da shirin ficewar Birtaniya daga kungiyar EU zai shafa.
Darajar kudin Birtaniya na "Pound Sterling" na tangal-tagal saboda halin tsaka mai wuya da Firaminista Theresa May ta shiga na rashin sanin tabbas game da makomar ta a fagen siyasa da kuma rashin sanin ko yarjejeniyar Brexit za ta samu amincewar majalisar dokokin Birtaniyar.
A ranaikun Alhamis da Jumma'a shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Turai za su yi taron koli a kan batun na ficewar Birtaniya daga kungiyar ta EU.