Birtaniya na da sauran aiki kan Brexit inji Merkel
September 25, 2018Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ba zai yiwu Birtaniya ta ce za ta zabi abinda ta ke so a huldar cinikayya da EU bayan ta fice daga kungiyar ba.
Shugabar gwamnatin ta ce Jamus za ta bujire wa dukkan wani yunkuri na yin kafar ungulu ga cinikayar kasa da kasa.
Angela Merkel ta baiyana hakan ne a wannan Talatar yayinda ta ke jawabi ga shugabannin kamfanoni da 'yan kasuwar Jamus a birnin Berlin.
Ta ce akwai bukatar Birtaniya ta tsaya ta yi tunani ta yanke shawarar abin da ta ke so a tattaunawar da ake yi na shirin ficewarta daga kungiyar EU.
Ta ce ina ganin jan lokaci ba zai taimaka wa tattalin arziki ba, ana bukatar su baje komai a faifai sannan a san yaya manufar dangantaka za ta kasance a gaba. A yanzu ana da makonni takwas zuwa goma wanda ya kamata a cimma matsaya kan shawarwarin. Abin da yake da muhimmanci shine me Birtaniya ke bukata.