Angela Merrkel ta zanta rikicin Isra'ila da Falastinawa
May 20, 2021Talla
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tattauna ta wayar tarho da Firaministan Falasdinu Mahmud Abbas a wannan Alhamis ta wayar tarho, da zummar duba yiwuwar cimma duk wasu hanyoyi na tsagaita wuta a batakashin da ake yi tsakanin Palasdinawa da Isra'ila.
Tun daga farko dai Merkel, ta bayyana cewa a share daya tana goyon bayan matakin Isra'ila na kare kanta, biyo bayan cinna rokokin da ta ce mayakan Hams na yi mata daga Gaza, a cewar wata sanarwa da kakakinta Steffen Seibert ya bayyanawa manema labarai.
Ko a wannan Alhamis Falasdinawa biyar aka tabbatar da sun hallaka, biyo bayan wani harin Isra'ila a yankin na Zirin Gaza.