1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel da batutuwan bashi da nukiliya na EU

March 25, 2011

Hanyoyin da za a bi domin ceto ƙasashen Turai da ke fama da matsin tattalin arziki na daga cikin al'amura da suka mamaye agendar taron Eu a birnin Bruxelles baya ga batu mai matiƙar sarƙaƙiya na makamashin nukiliya.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a taron Bruxelles na ranar juma'aHoto: dapd

shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana cewa takwarorinta na nahiyar Turai sun amince da shawarar duba lafiyar tasoshin makamashin nukiliya da suka mallaka, tare da sa ido akan su. Wannan mataki da suka ɗauka a taron ƙolin da suke gudanar a birinin Brussels na ƙasar Beljium, ya biyo bayan matsalar da ake fiskanta da tashar nukiliyar Fukushima dake ƙasar Japan bayan girgizar ƙasa da ta afku a cikinta. Jimillar tasoshin nukiliya guda 143 ne dai ƙasashen nahiyar ta Turai ta ƙunsa.

Sai dai fa a ɗaya hannu, matsalar bashi itace ta mamaye agendar taron na Eu na kwanaki 2. 'Yan siyasan na Turai dai sun ƙara amincewa da faɗaɗa shirin bayar da agajin gaggawa ga ƙasashen dake cikin wani hali na koma bayan tattalin arziki. shugabannin na Turai sun tabbatar da cewa za a fito da wata hanya ta bayar da agajin dindindin wacce zata maye gurbin wannan ta wucin gadi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar