1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata: Shekaru 100 na 'yancin zabe a Jamus

Yusuf Bala Nayaya
November 12, 2018

Ko da yake Merkel ta kasance shugabar gwamnatin Jamus mace ta farko, ta ce a majalisar dokokin Jamus mata na da kaso 30.9 cikin dari ne kawo yanzu abin da ke zama koma baya.

Festakt 100 Jahre Frauenwahlrecht
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana cewa akwai bukatar ganin an yi wasu abubuwa da dama wajen ganin an samar da daidaito tsakanin maza da mata a Jamus. Da take jawabi a wannan Litinin a wajen bikin tuni da shekaru 100 da mata suka fara samun 'yanci na fita kada kuri'a a Jamus Merkel, ta ce har yanzu sun gaza ganin shedu na damawa da mata a harkoki da suka shafi siyasa da harkokin kasuwanci da kimiya da al'adu.

Ko da yake Merkel ta kasance shugabar gwamnatin Jamus mace ta farko, ta ce a majalisar dokokin Jamus mata na da kaso 30.9 cikin dari ne adadin da ke zama koma baya idan aka kwatanta da kashi 36.5 a gwamnatin da ta gabata.

A cewar Merkel dai sun cimma nasarori da dama amma har kawo yanzu suna da sauran aiki, amma dai ba za su lamunci kaskanci ba.