1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Merkel ta yi wa Isra'ila alkawarin ci gaba da taimaka mata

October 11, 2021

Yayin ziyarar ban kwana da ta kai Isra'ila, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta shaida wa hukumomi a Isra’ila cewa Jamus za ta ci gaba da daukar nauyin batutuwa da dama da suka shafi kasar.

Kanzlerin Angela Merkel in Israel  Naftali Bennett
Hoto: Menahem Kahana/AP/picture alliance

Shugabar gwamnatin ta Jamus mai barin gado, Angela Merkel dai ta jaddada matsayin kasarta ne a game da tsaya wa Isra'ila a kan duk wani abu da ya shafi mutuncinta ta fuskar tsaro musamman a kowane hali.

A cewar Merkel batun kisan Yahudawa na Holocaust a lokacin yakin duniya na biyu, nauyi ne da ke kan Jamus kuma zai ci gaba da kasancewa a kanta tsawon lokaci na tarihi.

"Saboda kasancewar Isra'ila kasa mai bin tafarkin dimukuradiyya a lokacin da ake iya cewa babu dimukuradiyyar yadda ake so a tunaninmu, abu ne muhimmi mu kasance da kyakkyawar alaka a kan batutuwa da dama. Wannan ya hada da batun tsaro da muka yi magana a kai. Jamus za ta yi nazarin daukar nauyin Isra'ila kamar yadda Firaminista Naftali ya fadi. Batu ne na kiyaye daukar bangare, amma kuma akwai matsayarmu da ke a fili game da tsaron Isra'ila ala kulli halin."

Angela Merkel a ziyarar da ta kai wurin tunawa da kisan Holocaust a Birnin KudusHoto: Ilia Yefimovich/dpa/picture alliance

Shugabar gwamnatin ta Jamus Merkel ta ma ajiye furanni musamman domin tunawa tare da karrama Yahudawan da suka mutu sanadin kisan kiyashin na Holocaust.

A nashi bangare Firaminista Isra'ila Naftali Bennet, yabo ya yi ga irin rawar da Angela Merkel ta taka cikin shekarunta 16 na mulki, da ya ce gagaruma ce a fannin dawo da fahimtar juna ganin irin zaman doya da manja da aka yi saboda kisan 'yan Nazi a Jamus a shekarun na baya.

"Wadanda suka zabi zama 'yan kallo ko zama tsaka-tsaki a game da rikicin Isra'ila da kasashe irin su Iran da kungiyoyi kamar su Hamas da Hezbollah, na da ayar tambaya a kan mutuncinsu. Ke kuwa Angela Merkel, kin kasance haske abin koyi ga kasashen nahiyar Turai tsawon shekaru, musamman a kan duk wani batu da ya shafi goyon baya ga Isra'ila."

Firaministan Isra'ila Naftali Bennett da Angela Merkel a Birnin KudusHoto: Ariel Schalit/AP Photo/picture alliance

Wani bangare da bangarorin biyu suka tabo shi ne batun nukiliyar Iran da kuma bai wa Falasdinawa 'yancin kafa kasarsu. A nan ma ga abin da Merkel ke cewa:

"A wasu lokutan muna kin batun samar da kasar Falasdinu da za ta kasance mai cikakken 'yanci, amma fa a ganina ko ba komai za mu amince da samun a manufar da za ta samar da kasar Isra'ila da za ta dore a kan tafarkin dimukuradiyya."

A lokacin ziyarar Angela Merkel dai, shugabannin biyu sun gana da 'yan majalisar ministoci da ma wakilan kamfanoni a Isra'ilar.

Haka nan ma shugabar gwamnatin ta Jamus ta yi wata ganawa da shugaban kasar Isra'ila Isaac Herzog.

Shugaban na Isra'ila ya kuma karramata da digirin girmamawa a shahararriyar cibiyar bincike ta Weizmann Institute saboda kasancewarta macen da ta yi fice a fannin kimiyya a cibiyar, ya kuma kira ta kawar Isra'ila.

Haka zalika a lokacin ziyarar Angela Merkel ta samu wani digirin na girmamawa a wata cibiyar fasaha ta Haifa Technion-Israel Institute of Technology.