Merkel na son Jamus ta taka rawa a duniya
December 31, 2018.
Angela Merkel ta soma jawabin ne na sabuwar shekara da yin bita a game da tsawon lokaci mai sarkakiya da aka kwashe kafin kafa sabuwar gwamnatin hadaka bayan zaben shekara ta 2017. Lamarin da aka kwashe watannin shida ana jira, wanda aka yi ta samun sabani tsakanin 'yan jam'iyyar CDU da kuma CSU ta Horst Seehofer da kuma jam'iyyar 'yan girguzu ta SPD a kan batun 'yan cirani a Jamus.
Ta ce'' Ina tunanin yadda wannan shekara a fuskar siyasa ke karewa a maracen yau game da wahala da kuma gararin da muka sha a tsawon shekarar. Na san cewar da yawa daga cikinku gwamnatin hadakar ta zamemaku abin damuwa. Farko dai mun kwashe dogon lokaci kafin kafa gwamnati amma a fahimtata dimukaradiyyarmu ta ta'alaka ne bisa yarjejeniya kamar yadda muka cimma nasarar girka gwamnatin hadaka, wacce ke zaman tubali na hadin kan al'umma da zaman lafiya a kasarmu."
Shugabar gwamnatin wacce ke kammala aikinta a shekara ta 2021 ba ta son nuna cewar irin tarnakakin da ke tattare da kawance shi ne dalilinta na ja da baya, ta gwamace ta nuna cewar tsawon shekarun har 13 a kan harkokin siyasar sun isa zama hujjarta na bari a gajeta. Angela Merkel da ta itifakin cewar duk kalulalen da ake cin karo da su a yanzu abu ne da akan iya shawo kansu idan har ana aiki tare da hadin kai da wasu kasashen ketare mokobta: Kalubalen kuwa sune canjin yanayi, batun 'yan cirani da kuma ta'addanci
Ta ce. '' Muna yi koyi da wadanda suka gabacemu na tabbatar da cewar ba za mu iya shawo kan kalubalen da ke a gabanmu ba idan har ba mu kasance tsintsiya madarminkin daya tare da sauran kasashen ketare ba.''
Merkel na so Jamus ta taka rawa a duniya
Jamus wacce a ranar daya ga watan Janairun 2019 za ta kasance mamba a kwamitin sulhu na MDD na tsawon shekaru biyu, Angela Merkel ta ce wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da hulda ta kasa da kasa ta zamanto ba ta da tabbas. Ko shi ke ma ba ta bada misali ba, amma dai ta yi shaguben cewar aubuwan da ke faruwa na tayar da hankalinta, kuma ta ce za su kara a da himma a hanyoyin samun masalha tare da kara bada gudunmawar ayyukan jin kai. Sannan ta yi kira ga Jamusawa da su bada hadin kai na ganin Kungiyar Tarrayar Turai ta cimma muradunta a daidai lokacin da a ake shirin gudanar da zaben 'Yan majalisa naTuran a cikin watan Mayu mai zuwa.
Ta ce: '' Mun sha alwashin cewar kungiyar Tarrayar Turai za ta ci gaba da kasancewa karfaffa duk da ma cewar Birtaniya ta fice daga cikinta, amma za mu ci gaba da neman hanyoyin hulda domin bunkasar nahiyar ta Turai"
A karshe dai shugabar gwamnatin ta kammala jawabin ne da duba halin rayuwar al'umma a Jamus wanda ta ce suna ci gaba da yin aiki wurjajan domin inganta rayuar al'ummar