1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel na son tsaurara yaki da corona

Abdoulaye Mamane Amadou
December 9, 2020

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce yaduwar annobar corona tsakanin jama'a na daukar hankali, inda take duba yiwuwar kara tsaurara matakan yaki da corona.

Deutschland Bundestag Generaldebatte zum Bundeshaushalt
Hoto: Tobias Schwarz/AFP/Getty Images

A yayin ta gabata a gaban majalisar dokokin Jamus, Angela Merkel ta bukaci da a duba yiwuwar karfafa matakan dakile yaduwar annobar corona a Jamus, ciki har da da kara rage adadin wadanda ka iya haduwa wuri guda a gabanin bukukuwan Kiristmetin da ke tafe, da ma duba yuwuwar shiga hutun 'yan makaranta da wuri.

Haka shi ma ministan harkokin lafiyar Jamus ya bayyana muhimmancin daukar matakan yaki da annobar musamman ma a yankunan da aka samu mutun 200 daga cikin dubu 100 da suka kamu da annobar.