Merkel ta buƙaci samar da managarcin tsari domin shawo kan matsalar kudin euro
December 2, 2011Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kashedi da cewa za'a ɗauki shekaru mai tsawon kafin a iya shawo kan matsalar bashi da ta dabaibaye ƙasashen Turai masu amfani da kuɗin bai ɗaya na euro. Ta ce ƙasashen na buƙatar samar da wani jadawalin tattalin arziki da zai magance matsalolin kuɗin da suke fuskanta. Angela Merkel ta baiyana hakan ne a wani jawabi da ta yi a gaban majalisar dokokin Jamus domin baiyana matsayin ƙasar gabanin taron ƙolin ƙungiyar ƙasashen Turai da zai gudana a mako mai zuwa. " Ta ce idan har muna son maido da martabar mu to kuwa akwai buƙatar mutum ya yi tsai da hankalinsa ya daina kama jita-jita, ta haka ne za'a sami sahihiyar makama da kowa zai aminta da ita, A saboda haka ne muke buƙatar yin gyaran dokoki waɗanda za su ɗora Tarayyar Turai a kan kyakyawar turba domin wanzuwar cigaba mai dorewa".
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu