1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta danganta corona da masifar wannan karni

Binta Aliyu Zurmi
January 21, 2021

Shugabar gwamnati Angela Merkel ta kare tsauraran matakai da ta dauka don yaki da cutar corona, inda ta ce wannan annoba masifa ce a wannan karni kuma a halin yanzu Jamus na cikin halin "tsaka mai wuya". 

Deutschland Coronapandemie Pressekonferenz Bundeskanzlerin Angela Merkel
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture-alliance

A lokacin da take bayani ga manena labarai a birnin Berlin, shugabar ta ce duk da hadarin da ke tattare da rikidewa da kwayar cutar ke yi, ya kamata a guji rufe kan iyakoki da kasashen Turai da ke makwabtaka da Jamus. Sai dai ta bada shawarar hada gwiwa tsakanin kasashe dabam-dabam don yaki da annobar gadan-gadan. 

Sannan kuma ta ce da zaran an cigaba da samu raguwar masu kamuwa da coronavirus a Jamus, za a fara bude wuraren kula da yara da kuma makarantu.

Yanzu haka kasar ta Jamus na samu raguwa masu kamuwa da cutar a cewar cibiyar Robert Koch, cibiyar ta ce a cikin kwanaki bakwai kasar ta yi kasa sosai a yawan adadin da take samu, irinsa na farko tun a watan Nuwamba bara.

Jamus ta sha alwashi cin galabar wannan cutar kafin karshen wannan shekarar.