Merkel ta fuskanci koma baya na siyasa
July 18, 2010Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta sake fuskantar raguwar magoya bayanta sakamakon murabus na magajin garin Hamburg, Ole von Beust. Birnin Hamburg da ke zaman na biyu mafi girma a Jamus na ɗaya daga cikin jihohin ƙasar guda 16. Von Beust kamar dai Merkel mamba ne na jam'iyyar CDU da ya shafe shekaru kusan tara yana mulkin jihar ta Hamburg. Ya faɗa wa manema labarai cewa zai sauka daga muƙaminsa a ranar 25 ga wata mai zuwa, yana mai kafa dalilai na gaban kansa. Kenan shi ne na shidan shugabannin jihohi na jam'iyyar CDU da suka bar muƙamansu cikin watanni goma da suka gabata. Kafafen yaɗa labaran Jamus sun kira murabus ɗin na von Beust tamkar babban koma baya ga Merkel.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal