1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta taimaki yankunan da aka yi ambaliya

Abdoulaye Mamane Amadou
August 10, 2021

A yayin ganawarta da shuwagabannin jihohi 16 Angela Merkel ta ce gwamnati za ta ware euro miliyan dubu 30 domin sake gina wuraren da suka fuskanci ibtila'in ambaliya.

Berlin | Pressekonferenz zur Flutkatastrophe und Coronakrise: Angela Merkel
Hoto: CHRISTIAN MANG/REUTERS

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ce ta bayyana haka a yayin wata ganawar da ta yi da shuwagabannin jihohi 16 na kasar a wannan Talata, inda a taron manema labarunta shugabar gwamnatin ta ce  za a mika wa jihohin kudaden ne a matsayin gudunmawa.

Tun daga farko dai gwamnatin ta Jamus ta ware kudi har euro miliyan 400 a tsakiyar watan jiya a matsayin dauki ga wadanda ambaliyar ta yi wa mumunan illa. Kimanin mutun 190 ne dai suka hallaka sakamakon mummunan ambaliyar da ta fi yin muni a jihohin Rhein Platinat da Nord Rhein Westphaliya a tsakiyar watan Yuli.

A share guda kuma taron kolin da shugabar gwamnatin ta yi da ministocin jihohin 16, ya kuma ambaci dakatar da yi wa jama'a gwajin cutar corona kyauta, a wani yunkuri na kara jan hankalin jama'a da su ci gaba da yi alluran rigakafi.

Ö-Ton Merkel : Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kenan ke cewa "Tun da mun riga mun ba wa jama'a damar yin rigakafi kyauta, daga yanzu za mu dakatar da yin gwajin cutar kyauta ga wadanda ka iya yin rigakafin daga ranar 11 ga watan Oktoban wannan shekara."