1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta jaddada kalamanta kan daukar 'yan gudun hijira

August 26, 2025

Shekaru goma da suka gabata ne tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta yi mashahurin kalaminta na "Wir schaffen das” wanda ke nufin "Za mu iya yin haka.” dangane da karbar dubban 'yan gudun hijira.

Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel
Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus, Angela MerkelHoto: Reynaldo Paganelli/NurPhoto/picture alliance

Wannan maganar ta shafi yanke shawararta na karbar dubban 'yan gudun hijira zuwa Jamus a shekarar 2015.

A ranar Litinin, Merkel ta yi nazari kan wannan shawara, inda ta ce ta yi hakan ne bisa ga manufofin jinkai da darajar dan adam.

A lokacin da ta fadi wannan kalaman, an yi hasashen cewa za a samu isowar ‘yan gudun hijira kimanin dubu 800 a Jamus, mafi yawa da aka gani na tserewar jama'a daga yakin basasa mai tsanani a Siriya.

Angela Merkel ta amince da girman kalubalen da ake fuskanta, kuma ta nuna mamaki kan yawan suka da kalamanta suka jawo.

Duk da suka da suka sha, ta ce ba ta taba tunanin cewa Jamus ta kai ga hali na gajiyawa ba.

Tsohuwar shugabar gwamnatin ta Jamus Merkel ta tsaya kan shawarar a matsayin abin da ya dace ke nan na dabi'a.