1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karo na biyu Angela Merkel ta fuskanci rawar jiki a Barlin

Abdoulaye Mamane Amadou
June 27, 2019

A karo na biyu shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sake rawar jini lokacin da ta bayyana a bainar jama’a kwanaki bayan wani makamancin hakan da ya risketa bisa tsananin zafin da ake fuskanta yanzu a tarayyar Jamus.

Merkel hat erneut Zitteranfall
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

Jim kadan bayan shigowarta don jagorantar wani bikin bankwana ga tsohon ministan shari'a a birnin Berlin a wannan Alhamis, hoton bidiyon da aka dauka na bikin ya nuna yadda jikinta ke kadawa, a yayin da take kusa da shugaban kasar Jamus Frank Walter-Steinmeier.
Masu aiko da rahotanni sun ce sun ga Angela Merkel daram da kafafunta, tana takawa mintoci 30 bayan abin da ya faru a lokacin da ta isa a harabar majalisar dokokin Jamus ta Bundestag. Mai magana da yawun shugabar ya tabbar da cewa Merkel na nan daram, kana kuma za ta jagoranci rantsar da sabon ministan shari’ar kasar, ana kuma sa ran a karshen mako za ta halarci taron manyan kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya G20.