Merkel ta sauke shugaban hukumar leken asiri
September 18, 2018Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sauke shugaban hukumar leken asiri na cikin gida na kasa Hans-Georg Maasen daga mukaminsa inda aka yi masa sauyin wurin aiki.
A yanzu Maasen zai zama sakatare a ma'aikatar cikin gida ko da yake sauyin matsayin na zama tamkar ci gaba ne a gare shi.
Merkel ta dauki matakin ne domin kwantar da hankula kan takaddamar da ta taso game da batun ‘yan gudun hijira da masu kyamar baki, lamarin da a baya ya jefa gwamnatin hadin gwiwar Jamus din cikin halin tsaka mai wuya.
Tun da farko Jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta bukaci sallamar Maasen daga shugabancin hukumar leken asirin ta BfV sabanin muradun ministan cikin gida Horst Seehofer na jam'iyyar CSU da suke kawance a gwamnati.
Maasen mai shekaru 55 da haihuwa ya sami kansa cikin badakala ne bayan da yace yana da shakku kan gaskiyar rahoton da ke cewa masu tsattsauran ra'ayi da ‘yan Nazi sun rika kai harin kan mai uwa da wabi akan baki a garin Chemnitz a gabashin Jamus a karshen watan Augustan da ya gabata.