Merkel ta soki lamirin gwamnatin Turkiya
June 17, 2013Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta soki matakin ba sani ba sabo da 'yan sandar Turkiya ke dauka a kan masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a birnin Santambul da sauran biranen kasar. A wata hira da aka yi da ita gabanin ta tashi zuwa taron kolin kasashen Kungiyar G-8 a yankin Ireland ta Arewa, Merkel ta ce dole ne sabuwar kasar Turkiya ta amince cewar mutane na da 'yancin bayyana ra'ayinsu. Sai dai shugabar gwamnatin ta Jamus ta kauce daga amsar tambayar ko wannan matakin karfi da hukumomin na Turkiya ke dauka, ya dace wata kasa dake neman shiga Kungiyar Tarayyar Turai EU ta dauka. Shaidu sun rawaito cewa a cikin daren Lahadi zuwa safiyar Ltinin 'yan sanda a biranen Santambul da Ankara sun yi amfani da karfi fiye da kima a kan masu boren kin jinin gwamnati. Don nuna adawa da matakan da 'yan sandar ke dauka a kan masu zanga-zangar, manyan kungiyoyin kwadago biyu a kasar sun kira da a gudanar da yajin aiki. Sai dai ministan cikin gida ya kira matakin 'yan kwadagon da cewa haramtacce ne.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas