Merkel ta soki lamirin Putin na Rasha
December 8, 2014Talla
A cikin wata hira da ta yi da jaridar "Welt am Sonntag" da ake bugawa a kowace ranar Lahadi a Jamus, Angela Merkel ta soki shugaban Rasha Vladimir Putin da yin shisshigin a harkokin kasashen Moldaba da Jojiya da kuma Ukraine sakamakon yunkurin da suke yi na shiga cikin Kungiyar Gamayyar Turai.
Angela Merkel ta yi amfani da wannan dama wajen sukar manufofin tattalin arzikin Italiya da kuma Faransa, sakamakon karin wa'adi da kasashen biyu suka samu daga EU domin daidaita komadarsu ta tattalin arziki da ke tangal-tangal. Ita dai Faransa ta yi alkawarin rage bashin da ke kanta kafin shekara ta 2013. Sai dai kuma ta bayyana cewar ba za ta sami damar cika wannan alkawari kafin shekara ta 2017 ba.