Merkel ta yaba da ci-gaban da Girika ke samu na magance rikicin bashi
October 9, 2012A ziyarar da ta kai birnin Athens shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yaba da sauye sauyen farfaɗo da tattalin arziki a Girika sai dai ta yi kira da a ɗauki ƙarin matakai. Bayan tattaunawa da firaminista Antonis Samaras Merkel ta ce ra'ayinsu ya zo ɗaya game da abin da ya kamata a yi.
"Mun amince cewa dole ne matakan tsimin da ake ɗauka da kuma sauye sauyen tattalin arziki da jama'a ke tir da su, su kai ga bunƙasar tattalin arziki. Saboda haka za mu goyi da bayan dukkan matakan da suka dace domin buɗe wa Girika ƙofofin samun rance daga bankin zuba jari na Turai."
Merkel ta kuma yaba da jama'ar Girika bisa sadaukarwar da suka nuna. Shi ma a nasa ɓangare firaminista Samaras na Girika ya ce ƙasarsa za ta samu damar samun bashi daga hukumomin tallafi na duniya sannan za ta ci-gaba da zama a cikin ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman