1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta yi adabo da Roettgen

May 16, 2012

Za a maye gurbin ministan mahalli na Jamus sakamakon kayin da ya sha a zaben jihar Nordrhein- Westfalen(NRW)

Berlin/ ARCHIV: Bundesumweltminister Norbert Roettgen (CDU) geht in Berlin im Konrad-Adenauer-Haus zur Sitzung des CDU-Praesidiums (Foto vom 13.09.10). Norbert Roettgen tritt als Bundesumweltminister zurueck. Das erfuhr die Nachrichtenagentur dapd am Mittwoch (16.05.12) aus regierungsnahen Kreisen. Der 46-Jaehrige hatte als Spitzenkandidat der CDU bei der Wahl in Nordrhein-Westfalen eine historische Niederlage hinnehmen muessen. Seinen Rueckzug vom Amt des Landesvorsitzenden der nordrhein-westfaelischen CDU hatte Roettgen direkt nach der Wahl am Sonntag verkuendet. Bundeskanzlerin Angela Merkel (CDU) hat fuer 16.30 Uhr eine Erklaerung angekuendigt. (zu dapd-Text)
Hoto: dapd

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta sallami Norbert Roettgen daga mukaminsa na ministan mahalli. Hakan ya zo ne bayan da jam'iyyar CDU ta sha kayi a zaben majalisar jihar Nordrhein-Westfalen(NRW) inda Roettgen ya tsaya a karkashin tutarta. Shugabar gwamnatin ta ba da sanarwa hakan ne a wani taro manema labaru da ta shirya ba zato ba tsammani. Ta ce ta yi kira ga shugaban kasa, Joachim Gauck da ya sauke Roettggen daga mukaminsa ya kuma maye gurbinsa da Peter Almaier, mai kula da harkokin jam'iyyar CDU. Shi dai Roettgen mai shekaru 46 ya sha mugun kayi a zaben na Jihar NRW- kayin da ke zama irin sa mafi muni da CDU ta sha a tarihinta. Tuni ne dai bayan sanar da sakamakon zaben a yammacin Lahadin da ta gabata Roettgen ya sanar da murabus dinsa a matsayinsa na shugaban jam'iyyar a jihar NRW.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Zainab Mohammed Abubakar