1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta kare yarjejeniya kan ci-rani

Abdul-raheem Hassan MNA
July 4, 2018

A jawabin da ta yi a majalisa karon farko tun bayan takaddama da Seehofer, Merkel ta jaddada muhimmanci cimma matsaya guda.

Deutschland Haushaltsdebatte im Bundestag in Berlin
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gabatar da jawabi ga majalisar dokokin kasar ta Bundesta, a karon farko tun bayan da suka fara takun saka da ministan harkokin cikin gidan kasar, kuma shugaban jam'iyyar CSU, Horst Seehofer kan 'yan gudun hijira. Sai dai bisa ga dukkan alamu da sauran rina a kaba wajen cimma daidaito tsakanin jam'iyyun kawancen da ke shugabancin kasar.

Shugabar gwamnatin ta Jamus ta bayyana gaban majalisar domin bayyana karin wasu hujjoji kan manufofin da ta sa gaba, tare da ba wa kusoshin gwamnati damar tabka muhawara kan tsare-tsare da manufofin da gwamnatin ke tafiya a kai. Sai dai a irin wannan ganawar 'yan adawa na samun damar kalubalantar kudurorin gwamnati. Majalisar ta kaure da cece kuce kan kin amincewa da tsarin 'yan gudun hijira da ke barazanar durkusar da gwamnatin Merkel tare da raba kan jam'iyyar kawance da ke mulki.

Hada karfi don tinkarar matsalar 'yan gudun hijira

Daga hagu ministan cikin gida Horst Seehofer, ministan kudi Olaf Scholz sai kuma Angela MerkelHoto: picture-alliance/Anadolu Agency/A. Hosbas

Jawaban na Merkel gaban majalisar na zama wata dama a gareta wajen nuna ikon gwamnatinta tare da alfahari yarjejeniyar da ta cimma a makon da ya gabata a taron wasu shugabannin kungiyar tarayyar Turai kan 'yan gudun hijira.

"Yadda za mu tinkari tambayoyi masu cike da kalubale kan 'yan gudun hijira, hakan zai nuna ko kungiyar EU za ta ci gaba da wanzuwa."

Merkel ta kuma jaddada bukatar samar da tsaro a kan iyakokin Turai tare da cimma matsaya da kasashen Afirka wajen dakile kwararowar bakin haure zuwa Turai ta barauniyar hanya.

"Matsalar 'yan gudun hijira matsala ce ta duniya, wacce kuma ke bukatar hada karfi da karfe da sauran kasashen duniya wajen samar da mafita."

A yanzu haka dai shugabar gwamnati ta Jamus Angela Merkel, za ta ci gaba da tattaunawa da jam'iyyar kawance da ke cikin gwamnati ta SPD, a wani mataki na cimma yarjejeniyar karshe kan batun 'yan gudun hijira da ke neman zama karfen kafa a tsakanin jam'iyyun CDU da CSU da ke zaman abokan kawancen juna na fil'azan.