Merkel ta yi kira ga Birtaniya da kada ta fice daga tarayyar Turai
February 27, 2014Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga Birtaniya da kada ta fice daga kungiyar tarayyar Turai EU. A jawabin da ta yi a gaban majalisun dokokin Birtaniya a birnin London, Merkel ta ce sai an hada kai ne kasashen Turai za su yi karfi. Ta ce a cikin wannan duniya da ke kara hadewa, daidaikun kasashe a Turai ba za su iya samun wani angizo ba. Wannan kiran dai na da alaka da muhawarar da ake yi a Birtaniya game da yi wa kungiyar EU kwaskwarima da kuma yiwuwar ficewar Birtaniya din daga wannan tarayya. Merkel ta ce "dole kungiyar tarayyar Turai ta kara karfi, ta daidaita al'amuranta kana ta kara yin gogayya fiye da yanzu. Dole ta hada karfi waje guda kana ta fuskanci babban kalubalen da ke gabanta."
Tun gabanin wannan jawabi da ke zama irinsa na farko cikin shekaru 44 da wani shugaban gwamnatin Jamus ya yi a majalisar dokokin Birtaniya, Merkel ta yi nuni da bukatar Birtaniya na yi wa yarjeniyoyin EU gyaran fuska.
A nasa bangaren Firaministan Birtaniya David Cameron ya ce kasarsa da Jamus sun jaddada muhimmancin 'yancin Yukren a matsayin dunkulalliyar kasa. Yayin taron manema labarai albarkaci ziyarar da Angela Merkel ta kai birnin London, Firaministan Cameron ya ce dukkansu biyu sun goyi da bayan zaman Yukren a matsayin kasa daya al'umma daya.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman