1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ba za ta Amirka ba a saboda corona

May 30, 2020

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ba za ta birnin Washington kamar yadda Shugaban Amirka Donald Trump ya bukata ba.

Argentinien G20-Gipfel Angela Merkel und Donald Trump
Hoto: Getty Images/AFP/S. Loeb

Trump dai ya gayyaci shugabannin kasashe masu karfin masana'antu na duniya, G7, zuwa taro na zahiri a watan Yuni mai zuwa. Kafar yada labarai ta Politico ce ta ruwaito hakan. 


Sai dai Steffen Seibert mai magana da yawun shugabar gwamnatin Jamus ya ce ganin yadda annobar corona ke ci gaba da wanzuwa, Angela Merkel ba za ta je wani taro na zahiri a Amirka ba. Tun kafin yanzu ma dai Merkel din ta yi gargadin cewa zai zama anyi garaje idan har duniya ta fara gudanar da manyan taruka na zahiri a watan Yuni. 


To amma Firaministan Birtaniya  Boris Johnson ya nuna alamun goya wa Shugaba Trump  baya a kan wanann, inda Johnson ya ce idan dai har zai yi wu shi yana goyon bayan shugabannin duniya su taru a wuri guda kowa ya ga kowa.


Amirka dai ta samu masu coronavirus kusan milya daya da dubu dari bakwai yayin da Jamus ta samu mutum dubu dari da tamanin da uku.   A cikin wannan adadi corona ta kashe mutane fiye da 100,000 a Amirka yayin da cutar ta hallaka kasa da mutane 9,000 a Jamus.