1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel: Waiwayen baya da tsokaci kan Putin da Trump

Abdullahi Tanko Bala
November 21, 2024

A littafin da ta rubuta wanda za a kaddamar a kwanan nan tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi tsokaci kan tarihin rayuwarta da mulkin kama karya a duniya da kuma rikicin Ukraine

Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel Hoto: Bernd Von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta baiyana yadda dangantakarta ta kasance tsakaninta da shugabannin duniya kamar shugaban Rasha Vladimir Putin da Donald Trump a zamanin mulkinta na shekaru 16 a littafin da ta rubuta na waiwayen baya yayin da ta ke shan suka cewa ita ce ummul haba'isin rikicin da ake fama da shi a yanzu.

Merkel yayin da ta ke jawabi a Berlin a bikin cikar ta shekaru 70 da haihuwaHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

A ta'alikin da aka fitar gabanin kaddamar da littafin wanda za a yi a ranar 26 ga watan Nuwamba, Merkel ta tabbatar da kudirinta na kin amincewa Ukraine zama mamba a kungiyar kawancen tsaro ta NATO a taron kolin kungiyar da aka yi a 2008 a Bucharest wanda manazarta suka ce mai yiwuwa hakan shi ya hana Rasha kai wa Ukraine mamaya a wancan lokaci.

Angela Merkel da Donald TrumpHoto: picture-alliance/AP Photo/E. Vucci

Littafin na tarihin Merkel ya kuma nuna yadda ta nemi bai wa Paparoma shawara kan yadda zai yi mu'amala da Trump lokacin da aka zabe shi karon farko a matsayin shugaban Amurka, inda ta yi fatan shawo kan mutumin da ta lura yana da halayyar ya samu ko kuma a fasa kowa ya rasa, tare da kokarin jan hankalinsa ka da ya janye daga yarjejeniyar sauyin muhalli da aka cimma a Paris.