1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel za ta gana da Putin kan rikicin kasar Siriya

Ramatu Garba Baba
May 18, 2018

A wannan Juma'a, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta kai ziyara kasar Rasha inda za ta gana da shugaba Vladimir Putin, shugabanin biyu za su tattauna ne kan batun rikicin kasar Siriya.

Russland | Pressekonferenz Merkel Putin
Hoto: Getty Images/AFP/A. Nemenov

Wannan shine ziyarar Merkel ta farko a Rasha a shekara guda, bayan dan sabanin ra'ayi da aka samu a tsakanin kasashen biyu, bisa rawar da Rasha ke takawa a rikicin kasar Ukraine. Ana sa ran za su duba wasu batutuwa na cinnikaya a tsakaninsu da kuma batun matakin Amirka na soke yarjejeniyar da kasashen duniya shida suka kulla da Iran kan nukiliyarta.