Merkel zata gana da Dalai Lama duk da adawa da China ta nuna
September 23, 2007Talla
SGJ Angela Merkel zata ci-gaba da ganawa da Dalai Lama a fadar ta dake birnin Berlin kamar yadda aka shirya duk da adawa da haka da China ta nuna. A makon jiya gwamnatin China ta yi tir da taron kuma a dangane da haka ta kira jakadan Jamus a Beijing don ta nuna masa fushin ta a hukumance. Dalai Lama dai ya shafe sama da shekaru 50 yana gwagwarmayar nemawa yankin Tibet ´yancin cin gashin kai. Ganawar da zasu yi da Angela Merkel na zaman irinta ta farko da za´a yi tsakanin Dalai Lama da wani shugaban gwamnatin Jamus. Jami´an Jamus sun ce taron na musayar ra´ayoyi kawai kuma wani bangare ne na jerin tarurruka da Merkel ke gudanarwa da shugabannin addinai na duniya. Tuni dai China ta yi barazanar daukar mataki inda yanzu haka ta soke wani taron da aka shirya tsakanin manyan jami´anta da na Jamus a birnin Munich.