Merkel zata ziyarci yankin gabas ta tsakiya
January 3, 2007Talla
A farkon wata mai kamawa ne shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel zata kai rangadin aiki ayankin gabas ta tsakiya, abangaren manufofin kasar na bunkasa zaman lafiya a yankin ,ayanzu datake jagorantar sauran kasashen turai.Merkel zata ziyarci kasashen Masar da saudi Arabia da hadaddiyar daular larabawa da Kuwaiti.Kakakin ofishin ta ya sanar dacewa ,ziyarar ta sjugabar gwamnatin jamus zai farfado da daftarin suhun yankin,a karkashin jagorancin Eu da Rasha da Mdd da Amurka.A gobe nedai Angela Merkel zata isa birnin washinto,inda zata tattauna dangantakar kasuwanci tsakanin Amurka da kungiyar EU da shugaba George W Bush.