Merz ya bukaci amfani da dukiyar Rasha a tallafa wa Ukraine
December 5, 2025
Shugaban Gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya bukaci gwamnatin Belgium ta amince a yi amfani da kudaden Rasha da aka toshe don tallafa wa Ukraine.
Tun da farko, mai magana da yawun gwamnatin Jamus a Berlin ya sanar da cewa Merz ya soke ziyarar da ya shirya zuwa Norway domin ya samu damar tafiya Belgium don ganawa da Firaministan kasar Bart de Wever da Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen kan batun na Rasha da Ukraine.
Belgium za ta aikewa Ukraine jiragen sama na yaki guda 30
Merz ya ce, dole ne shugabannin Tarayyar Turai su cimma yarjejeniya da Belgium don amfani da kudaden Rasha da aka toshe don tallafa wa Ukraine.
Tattaunawar da za ta gudana yayin cin abinci a Brussels ranar Juma'a za ta mayar da hankali kan shawarar Hukumar Turai ta amfani da dukiyar Rasha da aka rike a cikin EU domin tallafa wa Ukraine.
Shugabanin Duniya na ci gaba da yin tir kan harin Brussels
An kiyasta cewa akwai kudaden Rasha da suka kai kusan yuro biliyan 185 a Belgium kadai wadanda yanzu haka ake rike da su.