1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merz ya caccaki Rasha a kan yakin Ukraine

February 23, 2026

Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz ya bukaci a kara matsa lamba ga Rasha domin ta kawo karshen yakin Ukraine.

Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz
Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich MerzHoto: Markus Lenhardt/dpa/picture alliance

Kalaman shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz na zuwa ne kwana guda gabanin cika shekara hudu da Rasha ta kaddamar da mamaya a Ukraine. Shugaban ya bayyana cewa dole ne Rasha ta fahimci cewa ba za ta iya samun karin yankuna ba. Merz ya kuma caccaki shugabancin Rasha, inda ya zargi gwamnatin Moscow da rashin mutunta hakokkin bil adama. Ya kuma kara da cewa Shugaba Vladmir Putin ba zai kawo karshen yakin ba ko da kuwa da Ukraine ta mika wuya.

Karin bayani:Merz ya bukaci amfani da dukiyar Rasha a tallafa wa Ukraine 

Jamus ta kuma yi alkawarin ci gaba da tallafa Ukraine da kayan yaki. A cewar shugaban gwamnatin, kasar ta ba da tallafin dala biliyan 40 ga fararen hulda da kuma dala biliyan 50 na kayan yaki tun farkon fara yakin. Kawo yanzu Jamus ita ce kasar da kunshin tallafinta ga Ukraine ya fi na kowace kasa yawa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani