1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merz ya yi gargadi kan salon mulkin danniya

Abdullahi Tanko Bala
January 22, 2026

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya yi kashedin cewa sabon salon taku na siyasar duniya na kara baiyana cikin hanzari kuma wanzuwar nuna karfin iko na da matukar hadari ga duniya

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz a taron Davos
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz a taron DavosHoto: Fabrice Coffrini/AFP/Getty Images

Da yake jawabi a taron tattalin arzikin duniya a Davos, Merz ya yi nuni da yakin Rasha a Ukraine da kara tasowar China da kuma Amurka da ke kara sauya fasalin harkokin waje da manufofin kan tsaro a duniya.

Merz yace Jamus ta bi irin wannan tafarki a baya amma bai yi mata kyau ba a karni na 20. Yace irin wannan mataki na mayar da duniya baya.

Ya ja hankali da cewa karfin tasiri dama ce ta hada hannu sauran kasashe domin kulla kawance da martaba juna cikin girma da arziki.