Merz yace shigar Ukraine Tarayyar Turai yana da muhimmanci
April 27, 2026
A yayin wata tattaunawa da ɗaliban makarantar sakandare a garin Marsberg, Mista Merz ya yi fatan wata rana za a cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha, amma kuma ya yi nuni da cewa zai yiwu wasu sassan Ukraine su fita daga hannunta bayan yarjejeniyar.
A gefe guda kuma, Friedrich Merz ya yi tsokaci kan rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran, inda ya ce Amurka na fuskantar yanayi na shiga kunya a wannan rikici domin Iran ta fi ƙarfin yadda aka yi zato, kuma Amurkar ba ta da cikakkiyar dabarar shawo kan matsalar.
Merz ya bayyana cewa halin da ake ciki rikice ne sosai, kuma yana shafar tattalin arzikin duniya, ciki har da na Jamus. Amma duk da hakan a cewarsa, a Jamus shirye take ta taimaka wajen tsabtace ma’adanan ruwa domin sake buɗe mashigar Hormuz, muddin aka dakatar da wannan tashin hankali.