1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniArgentina

Messi ya yi bankwana da tawagar Argentina

October 7, 2026

Fitaccen dan wasan Argentina Lionel Messi, ya buga wasansa na karshe da tawagar kasar, bayan shafe shekaru 21 yana taka muhimmiyar rawa a gasanni dabam-daban.

Messi, yayin da yake bankwana da tawagar Argentina
Messi, yayin da yake bankwana da tawagar ArgentinaHoto: Gustavo Garello/AP Photo/dpa/picture alliance

Zakaran duniya kuma wanda ya lashe gasar Copa America har sau biyu Lionel Messi, ya buga wasansa na 208 kuma na karshe tare da tawagar Argentina, a wasan sada zumunta da kasar ta doke jamhuriyar Benin ci 3-0.

A yayin wasan da aka fafata a filin wasa na El Monumental, Messi ya kuma zura kwalonsa ta 126 da tawagar Argentina, sannan ya taimaka an ci kwallo biyu da suka ba wa Albiceleste nasarar a daren Talata.

Filin wasa na El Monumental da ke birnin Buenos Aires, ya yi cikar kwari da dubban masoyan Messi, domin shaida wannan rana mai cike da tarihi. 

Bayan tashi daga wasan Messi, ya bayyana cewa ''taka wa Argentina leda ya kasance babban abin alfahari a gare shi'', sannan ya yi godiya kan wannan dama da kasar ta ba shi.

Shin ya Argentina za ta kasance bayan Messi?

Messi mai shekaru 39, wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or har sau takwas ya shafe shekaru 21 yana taka wa tawagar Albiceleste ta Argentina leda, sannan ya kafa babban tarihi a kungiyar Barcelona.