1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Messi ya kamu da corona

January 2, 2022

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta sanar da cewa gwajin cutar coronavirus ya tabbatar da cewa shahararran dan wasanta Lionel Messi da wasu 'yan wasa uku sun kamu da cutar. 

Fußball Ligue 1 PSG v Nantes | Tor Messi
Hoto: Matthieu Mirville/Zuma/imago images

Sauran 'yan wasan sun hada da mai tsaron gidan kungiyar Juan Bernat da mai tsaron raga Sergio Rico da kuma dan wasan tsakiya Nathan Bitumazala.

Tuni dai 'yan wasan suka killace kansu don gudun yada cutar. Hakan dai na nufin cewa Mess ba zai taka leda a gobe Litinin ba a Faransa da ma wasan farko bayan hutu na kungiyar PSG a ranar Lahadi mai zuwa.