Messi zai koma Inter Miami na Amirka
June 8, 2023Talla
Fitaccen dan wasan kwallon kafa Lionel Messi zai fara taka leda a kungiyar Inter Miami da ke Florida na kasar Amirka. Zakaran kwallon duniya dan asalin Ajentina ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da jaridun da ke kula da lamuran wasanni na kasar Spain, bayan da ya yanke shawarar cewa ba zai koma FC Barcelona ba.
Shi dai Lionel Messi mai shekaru 35 da haihuwa ya buga wasansa na karshe a Paris St. Germain a karshen makon da ya gabata. Sai dai a baya-bayan nan, an yi ta cece-ku-ce kan wani yunkuri zuwa kasar Saudiyya don buga kwallo da zummar samun makudan kudade. Amma a kungiyar Miami, Messi zai samun kwatankwacin Euro miliyan 200 a kakar wasanni hudu.