Ana farautar wadanda suka kai hari gidan rawa
March 9, 2019Talla
Tuni aka baza jami'an tsaro don farautar wadanda suka kai harin na wannan Asabar. Hoton bidiyon da aka dauko na ginin, ya nuna yadda 'yan bindigan da aka fi sani da Sunrise da suka kuma yi kaurin suna a fataucin man fetur ne suka kai harin.
Shugaba Lopez Obrador da ya dare mulkin kasar a watan Disambar bara, ya gaji tarin matsaloli na 'yan daba da masu safarar miyagun kwayoyi, sai dai ya sha alwashin ganin bayan wadannan matsalolin bayan da ya sha ranstuwar kama aiki.