Mexico ta cafke fitaccen dan simogan kwayoyi
February 23, 2014Talla
Jami'an tsaron kasar Mexico sun cafke daya daga cikin mutanen da aka fi nema a duniya kan safarar miyagun kwayoyi, Joaquin Guzman, wanda ya yi kaurin suna wajen tsallakawa da kwayoyi daga kasar zuwa cikin kasar Amirka. Don haka yake cikin jerin mutennen da kasar ta Amirka ta fi nema babu kama hannun yaro
Cikin shekara ta 2001 Guzman ya tsere daga gidan fursuna, kuma an samu nasarar sake kama shi da taimakon jami'an kasar Amirka.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman