Tattalin arziki
Mexiko ta mika wuya kan hana bakin haure shiga Amirka
June 8, 2019Talla
Kasashen Amirka da Mexiko sun cimma yarjejeniya lamarin da ya kawar da saka kudaden fito ga kayayyakin da Mexiko ke kai wa zuwa Amirka. Karkashin yarjejeniyar Mexiko ta amince ta dakile bakin haure masu shiga Amirka, galibi daga kasashen Guatemala, Honduras da El Salvador masu fama da tashe-tashen hankula, inda za su zauna a Mexiko har zuwa lokacin da aka tantance takardunsu na neman mafaka a Amirka.
Sakamakon wannan yarjejeniya an soke shirin Shugaba Donald Trump na Amirka na fara karban kudaden fito kan kayyakin Mexiko masu shiga Amirka daga ranar Litinin mai zuwa.