1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Michel Barnier ya zama sabon Firaministan Faransa

September 5, 2024

Zaben Barnier a matsayin sabon firaminista ya biyo bayan murabus din tsohon mai rike da mukamin ne Gabriel Attal.

Sabon Firaministan Faransa Michel Barnier
Hoto: Emmanuel Dunand/AFP/Getty Images

A ranar Alhamis ne shugaban kasar Faransa Emmanueal Macron ya sanar da sunan tsohon mai shiga tsakani kan ficewar Burtaniya daga Tarayyar Turai Michel Barnier a matsayin sabon firaminstan kasar.

Sanarwar ta zo ne kusan wata biyu na rudanin siyasa da Faransa ta fada ciki biyo bayan zaben gaba da wa'adi na majalisa da shugaba Macron ya kira.

Faransa: Zagaye na biyu na zaben 'yan majalisar dokoki

Bernier mai shekara 73 zai kasance firaminista mafi tsufa a tarihin Faransa tun a tsaskanin shekarun 1453–1789 da kasar ta sabunta tsarin mulkinta.

Sabon firaminstan ya na da aikin tabbatar da samar da gwamnati da ta kunshi dukkan bangarorin siyasa domin kauce wa sabanin siyasa da ake fama da shi.

Faransa ta zargi IS game da harin Rasha

Tun a ranar Laraba ne 'yan siyasa da kafafen yada labarai a Faransa suke nuna yiwuwar sanar da sabon shugaban gwamnati wanda zai maye gurbin Gabriel Attal bayan zaben watan Yuli da ya haddasa gibi a majalisar kasar.