1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mike Pompeo zai ziyarci Jamus

May 24, 2019

Hukumomi a Jamus sun bayyana ranar da Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo zai ziyarci kasar bayan soke ziyararsa tun da fari a farkon watan nan.

Russland Sotschi | Treffen Mike Pompeo, Außenminister USA & Sergej Lawrow
Hoto: Reuters/P. Golovkin

Hukumomi a nan Jamus sun bayyana Juma'ar makon gobe, a matsayin ranar da Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo zai ziyarci kasar, bayan dage ziyarar da tun da fari aka tsara a farkon watan nan.

Yayin ziyarar ta aiki, ana sa ran Mike Pompeo zai tattauna da Shugabar gwanati Angela Merkel kan wasu muhimman batutuwa na diflomasiyya, musamman rikicin nan na mallakar makamashin nukiliyar Iran.

An dai dage ziyarar ta farkon ne, a ba zata, saboda dalilan da aka danganta da wata ziyarar da Mr. Pompeo zai kai kasar Iraki.

Mai magana da yawun Shugabar gwamnatin Jamus na cewa ganawar manyan biyu a Juma'ar da ke tafe, zai kuma yi nazarin wasu batutuwa da suka shafi yadda za a warware matsaloli a yankin gabas ta tsakiya.