1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Miliyoyin musulmi sun hau Arfa

August 10, 2019

Miliyoyin musulmi ne a yau ke kan dutsen Arfa don gudanar da muhimmiyar ibada bisa tafarkin addini na biyu mafi yawan al'uma mabiya a fadin duniya.

Saudi-Arabien Hadsch-Wallfahrt in Mekka
Hoto: picture-alliance/dpa/CIC

Kimanin Musulman miliyan biyu da rabi ne ke tsayuwar ta Arfa a kokarin cika daya daga cikin shika-shikan addinin Islama.

Aikin Hajji dai aikin ibada ne mafi girma da ke hada al'uma lokaci guda a duniya, wanda ake son musulmi ya yi shi akalla sau guda a rayuwarsa, muddin yana da halin saukewa da kuma koshin lafiya.

Lokacin tsayuwar dai ana addu'o'i ne da kuma karatun Alkur'ani mai tsarki.

Dubban jami'an tsaro ne hukumomin Saudiyya suka baza saboda tabbatar da tsaro lokacin aikin Hajjin na bana.

An kuma dauki matakan sanyaya wurare saboda cunkoson jama'a a yanayi na zafin da ake famaa da shi wanda haura makin digiri 40 a ma'aunin celcius.