1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Miliyoyin yara na shakar gurbatacciyar iska

October 31, 2016

A wani rahoton da hukumar kula da kanana yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta ce akwai kananan yara miliyan 300 da rayuwarsu ke fuskantar barazanar shakar gurbatacciyar iska.

Eritrea Kinder im Flüchtlingslager in der Region Tigrai Äthiopien
Hoto: Reuters/T. Negeri

Binciken rahoton dai ya nuna cewa irin iska maras tsabta da kananan yaran ke rayuwa a ciki na da mummunar illa da ke haifar da babbar matsala ga kwakwalwar wanda ke yin nakasu ga wasu sassa na halittun jikin yara.

A yanzu dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana samun yaro guda cikin bakwai a fadin duniya da ke shakar gurbatacciyar iska mai dauke da guba sabanin tsarin da ya dace da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO. Wannan ya sa ake ganin gurbatar yanayi a matsayin abin da ke zama barazana ga rayuwar kananan yara a duniya.

Binciken dai ya nuna cewa yara miliyan 520 a kasashen Afirka da ke fuskantar matsalar gurbatar yanayi na hayakin ababen hawa, da na murhun abinci hade da na kura mai datti da ma dumamar juji.