1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan cikin gidan Ukraine ya rasu a hadarin Helikopta

Abdullahi Tanko Bala
January 18, 2023

Ministan cikin gidan Ukraine Denys Monastyrskyi na cikin mutane 18 da suka rasu a hadarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya fado a wannan Laraba kusa da wata makarantar renon yara a wajen Kyiv.

Ukraine Kiew - Browary | Absturzstelle Hubschrauber mit Innenminister Denys Monastyrskyj
Hoto: Daniel Cole/AP Photo/picture alliance

Wasu yara kanana su uku na daga cikin wadanda suka mutu. Mutane 29 suka sami raunuka wadanda suka hada da kananan yara 15 kamar yadda ma'aikatar cikin gidan ta sanar.

Bugu da kari wani mataimaki ga ministan cikin gidan Yevhen Yenin na daga cikin wadanda aka bada sanarwar sun rasu a hadarin jirgin.

Bayanai da ke fitowa sun ce jirgin kirar Airbus H225 hukumar kula da sararin samaniya ta tarayyar Turai ta dakatar da amfani da shi na wucin gadi tun a shekarar 2016 saboda matakan kariya.