SiyasaGabas ta Tsakiya
Ministan harkokin wajen Isra'ila ya kai ziyara Somaliland
January 6, 2026
Talla
Duk da ci gaba da daukanta da Somaliya ke yi a matsayin wani yankinta, amma ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Saar ya isa Somaliland a wannan Talatar, kasa da makonni biyu bayan da kasarsa ta amince da kasar da ta ayyana kanta a matsayin 'yantanta.
Sanarwar da ta fito daga fadar shugaban kasar Somaliland ta ce tawagar ta Isra'ila ta sauka a Hargeisa babban birni, inda jami'an gwamnatin Somaliland suka tarbe ta a filin jirgin sama.
Karin bayani: Habasha za ta amince da 'yancin Somaliland
Ita dai Isra'ila ta amince da Somaliland a hukumance a ranar 26 ga Disamban 2025 a matsayin kasa mai cin gashin kanta, mtakin da ke zama farau tun bayan ballewarta daga Somaliya a shekarar 1991.