Ministan harkokin wajen Jamus a Yankin Gabas ta Tsakiya
February 2, 2012Babban abin da ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ke fatan gani shi ne sake farfaɗo da shawarwarin zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya. Hakan kuwa abi ne dake buƙatar tuntuɓar Palasɗinawa da Isra'ila. A sakamakon haka ministan harkokin wajen ya kai ziyara ta kwanaki biyar ga yankin gabas ta tsakiya, inda bayan ya da zangon da yayi a Ramalla ya kuma kai ziyara yankin Yad Vashem da aka tanadar don tunawa da ta'asar kisan kiyashi akan Yahudawa a Isra'ila.
A cikin wani bayanin da yayi ministan harkokin wajen na Jamus Guido Westerwelle ya ce ana baƙin ƙoƙari wajen shawo kan sassan biyu na Isra'ila da Palasɗinawa da su ci gaba da shawartawa da juna bisa manufar cimma daidaituwa akan shawarar ƙirƙiro wata ƙasa ta Palasɗinu mai cikakken ikon cin gashin kanta. Westerwelle ya ƙara da nuna ƙwarin guiwarsa duk da tafiyar hawainiyar da ake samu a shawarwari tsakanin Palasɗinawan da Isra'ila, kamar yadda ya nunar a cikin wata hira da tashar Deutschlandfunk tayi da shi safiyar yau alhamis:
"Mun tattauna akan maganar samar da ƙasashe biyu kafaɗa-da-kafaɗa da juna. Muna buƙatar ganin ƙasashe biyu masu girmama juna tare da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki. A saboda haka wani abu mai muhimmanci shi ne kada mu yi sake maganar gina ƙasar Palasɗinu ta zama ta fatar-baka kawai, a sakamakon haka muka kafa wata hukuma ta tuntuɓar juna tsakanin mahukuntan Jamus da na Palasɗinawan akai-akai."
A ganawar da suka yi tare da ministan tsaron Isra'ila Ehud Barak a safiyar alhamis ministan harkokin wajen na Jamus ya bayyana adawarsa da shawarar ɗaukar matakan soja akan ƙasar Iran, sannan ya ce abu mafi alheri shi ne a ci gaba da yi wa ƙasar matsin lamba ta ƙaƙaba mata matakai na takunkumi. Kazalika a karon farko Westerwelle ya fito fili yana mai tofa albarkacin bakinsa akan halin da ake ciki a Siriya ba tare da wata rufa-rufa ba, inda ya ce wajibi ne shugaba Bashar Assad ya fara share hanyar kafa wata gwamnati ta riƙon ƙwarya a cikin ruwan sanyi. Wajibi ne kazalika ya dakatar da matakansa na danniya da muzantawa. A wani abin dake zaman ƙara ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin Jamus da Isra'ila Westerwelle ya kai ziyara Yad Vashem, dandalin da aka tanadar don tunasarwa da ta'asar kisan kishin da 'yan Nazin-Hitler suka yi wa Yahudawa. Ma'aikatar harkokin wajen Jamus nan gaba zata riƙa tallafa wa kafar da kuɗi euro miliyan ɗaya a kowace shekara:
"Hakan ba kawai tana da nufin haƙiƙancewa ne daga ɓangaren gwamnati ba, wata shaida ce ta irin zumuncin da Jamusawa ke nunarwa ga al'umar Isra'ila dangane da alaƙar dake tsakaninsu. Ba zamu yi watsi da alhaki na tarihin da ya rataya a wuyanmu ba kuma a saboda haka muke madalla da abubuwan masu tunasarwa saboda zama darasi ga zuriya ta gaba."
A baya ga Isra'ila da Palasɗinu dai, ministan harkokin wajen na Jamus kazalika ya ziyarci ƙasashen Jordan da Masar a bulaguron nasa na kwanaki biyar ga yankin gabas ta tsakiya.
Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal
Edita: Muhammed Nasiru Awal