1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Ministan lafiya ya kamu da COVID 19

Zainab Mohammed Abubakar
October 21, 2020

Da ranar Larabar nan ce (21.10.20) aka tabbatar da cewar Jens Spahn ya kamu da cutar corona, kuma tuni ya dauki matakin kebe kanshi.

Jens Spahn | Gesundheitsminister Deutschland Mundschutz
Hoto: Markus Schreiber/Reuters

Mai shekaru 40 da haihuwa, Mr Spahn ya fara ne da jin alamun mura kafin ya je gwajin da ya tabbatar da cewar ya kamu da cutar. Tuni aka sanar da dukkan mutanen da suka yi mu'amala da shi.

Kakakin gwannati ya shaidar da cewar ministan lafiyan na Jamus, ya halarci taron majalisar zartarwar kasar da safiyar yau, sai dai babu bukatar sauran ministocin da suka halarci taron su kebe kansu, saboda yanayin katafaren wurin taron da kuma dokar sa tazara da ke tsakanin kujerun.