1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Mota da sufuri

Hadarin jiragen kasa ya tilas minista ajiye aiki

Suleiman Babayo LMJ
March 1, 2023

Ministan sufurin Girka Kostas Karamanlis ya ajiye aiki bayan hadarin jiragen kasa biyu da suka yi taho mu gama da juna inda mutane 36 suka halaka.

Girka
Kostas Karamanlis ministan sufurin Girka da ya ajiye aikiHoto: AP

Ministan sufurin kasar Girka, Kostas Karamanlis, ya mika takardar ajiye aiki a wannan Laraba sakamakon hadarin jiragen kasa biyu da aka samu wadanda suka yi taho mu gama da juna inda kimanin mutane 36 suka halaka, kana wasu da 85 suka jikata. A takardar ministan ya ce ajiye aikin shi ne girmama mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon wannan hadarin na sanyin safiyar wannan Laraba.

Firaminista Kyriakos Mitsotakis na kasar ta Girka ya kai ziyara inda aka samu hadarin kuma ya yi alkawarin daukan matakan ganin ba a sake samun irin wannan hadari na jirgin kasa a kasar ba.