1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan tsaron Jamus na ziyara a Nijar

Ahmed Salisu
December 19, 2023

Ministan tsaron Jamus Boris Pistorious ya fara wata ziyara a Nijar inda ake sa ran zai tattauna da jagorin gwamnatin mulkin sojin kasar da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

Niger Deutschland Verteidigungsminister Boris Pistorius
Hoto: Gazali Abdou/DW

Mr. Pistorious dai shi ne ministan Jamus na farko da ya ziyarci Nijar din tun bayan juyin mulki da aka yi, kuma ana sa rana zantawar da zai yi da mahukuntan na Nijar za ta tabo batutuwa musamman ma dai halin da kasar ke ciki.

Har wa yau, miinistan zai kai ziyara ga sojin Jamus kimanin 100 da ke girke a wani sansanin soji da ke wajen Yamai fadar gwamnatin kasar, sannan ana sa ran zai yi jawabi kan makomar sansanin.

Gabannin juyin mulkin da sojin suka yi dai, Nijar na kan gaba cikin kasashen Afirka da ke hulda da kasashen yamma wajen magance kwararar 'yan gudun hijira zuwa nahiyar Turai ta barauniyar hanya.