1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta ce Ukraine za ta galaba kan kutsen Rasha

Binta Aliyu Zurmi SB
February 18, 2023

Mahalarta taron tsaro da ke gudana a birnin Munich na Jamus suna ci gaba da tattaunawa kan lamuran tsaro a dauniya inda yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine yake daukan hankali.

Jamus | Taron tsaro na birnin Muich | Boris Pistorius
Boris Pistorius, Ministan Tsaron JamusHoto: Sven Hoppe/dpa/picture alliance

A ci gaba da halartar taron tsaro na shekara-shekara da ke gudana a birnin Munchen na kasar Jamus da shugabannin kasashen duniya ke yi, ministan tsaron Jamus Boris Pistorious ya yi gargadin cewar samun nasarar a yakin da Rasha ke yi da Ukraine na nufin ba shi damar mamaye wasu kasashe bayan Ukraine.

Pistorious a jawabinsa ga zauren taron ya bayyana alkawarin da kasarsa Jamus da sauran kawayen Ukraine suka yi na ci gaba da tallafa masu har sai sun kai karshen wannan mamayar duk tsawon lokacin da hakan zai dauka.

Ministan tsaron na Jamus, wanda ya kama aiki a watan da ya gabata ya kara jaddada bukatar kasashen duniya na yin duk mai yiwuwa na ganin Putin bai yi nasara a wannan yakin ba. A farkon wannan makon minista Pistorious ya amincer da karin manyan makamai ga Ukrain domin kare kanta.